Isa ga babban shafi
Jarida-Intanet

Shafukan intanet na jaridun duniya sun dauke

Shafukan intanet na wasu manyan jaridun duniya sun fuskanci kalubale na rashin aiki, bayan da suka dauke gaba daya. Kazalika matsalar ta shafi wasu shafukan sada zumunta.

Daukewar ta dakatar da ayyukan gidajen jaridun duniya
Daukewar ta dakatar da ayyukan gidajen jaridun duniya AP - Pavel Golovkin
Talla

Rahotanni sun ce, wannan al’amarin ya taba shafin gwamnatin Birtaniya, wanda hakan ya tsayar da shi cak.

Shafukan da lamarin ya shafa na nuna: "Error 503 Service Unavailable".

A cewar rahotannin farko, lamarin ba ya rasa nasaba da 'Fastly,' wato wani kamfanin rumbun adana bayanan intanet wanda ke samar wa da manyan kamfanoni shafin intanet.

Shafin intanet na New York Times, ya nuna cewa akwai matsala, sai dai daga bisani ya koma yadda yake. Haka ma abun ya kasance a shafukan BBC Guardian da Financial Times da Independent kafin daga bisani komai ya dai-daita.

Kodayake yanzu haka 'Fastly' ya ce yana bincike kan matsalolin game da tsarin gudanar da ayyukansa na duniya baki ɗaya.

Rahotannin baya-bayan nan na cewa, shafukan na intanet sun fara aiki sannu a hankali bayan daukewarsu baki daya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.