Isa ga babban shafi
G7 - Tattalin Arziki

Kasashen G7 za su raba tallafin rigakafin Korona biliyan 1

Shugabannin kasashen G7 dake taron kwanaki 3, za su cimma matsayar hada gwiwa wajen kara yawan alluran rigakafin Korona ta yadda za a iya samar da akalla biliyan 1 da za za su tallafawa kasashen duniya.

Tambarin kungiyar kasashen G7 masu karfin tattalin arziki a duniya dake soma taro yau Juma'a a Birtaniya.
Tambarin kungiyar kasashen G7 masu karfin tattalin arziki a duniya dake soma taro yau Juma'a a Birtaniya. Getty Images - Hugh R Hastings
Talla

Birtaniya dake zama mai masaukin baki ce ta sanar da shirin raba tallafin alluran rigakafin na Korona biliyan 1 a fadin duniya nan da shekarar 2023, inda ta yi alkawarin ita kadai za ta raba tallafin alluran da adadinsu ya kai miliyan 100 a cikin shekarar mai kamawa ta 2022, yayinda kuma nan da makwanni za ta soma raba sunkin alluran miliyan 5.

Ba ya ga batun yaki da annobar ta Korona da kuma daidaito wajen rabon alluran rigakafin  cutar tsakanin kasashe masu arziki da matalauta, ana sa ran taron kasashen na G7 zai Karkare tattaunawa kan kudurin yankawa manyan kamfanonin fasahohin zamani na Apple, Amazon, Facebook da kuma Google, biyan tarar kasha 15 na jumillar ribar da suke samu a shekara, kamar yadda shugaban Amurka Joe Biden ya nema.

Shugabannin na G7 za kuma su tattauna kan halin da ake ciki dangane da kokarin shawo kan matsalar sauyin yanayi.

Karo na farko kenan da shugabannin kasashen G7 ke haduwa keke da keke cikin kusan shekaru 2, tun bayan taron da suka yi a Faransa cikin watan Augustan 2019, lokacin da ake fama da rigimar tsohon shugaban Amurka Donald Trump kan huldar kasuwanci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.