Isa ga babban shafi
Isra'ila - Siyasa

Majalisar Isra'ila ta kawo karshen mulkin Netanyahu

Dubban mutane sun shafe sa’o’I suna kade kade da bushe bushe a Tel Aviv babban birnin Isra’ila, domin murnar kawo karshen mulkin Fira Minista Benjamin Netanyahu da Majalisar dokokin kasar ta yi, bayan da ya shafe shekaru 12 yana jagorantar kasar.

Masu bikin murnar kawo karshen mulkin tsohon Fira Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu a birnin Tel Aviv. 13/6/2021.
Masu bikin murnar kawo karshen mulkin tsohon Fira Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu a birnin Tel Aviv. 13/6/2021. JACK GUEZ AFP
Talla
Naftali Bennett sabon Firaministan Isra'ila, bayan nasarar da yayi a zaben da zauren majalisar dokokin kasar ta yi tsakanin gwamnatinsa ta hadin gwiwa da kuma tsohon Firaminista Benjamin Netanyahu.
Naftali Bennett sabon Firaministan Isra'ila, bayan nasarar da yayi a zaben da zauren majalisar dokokin kasar ta yi tsakanin gwamnatinsa ta hadin gwiwa da kuma tsohon Firaminista Benjamin Netanyahu. REUTERS - RONEN ZVULUN

‘Yan majalisa 60 ne suka kada kuri’ar zaben sabon kawancen ‘yan adawa karakshin jagorancin Naftali Bennet da kuma Yair Lapid da za su kafa sabuwar gwamnati, yayin da 59 suka zabi Firaminista Netanyahu.

A karkashin wannan sabon kawancen, Naftali Bennett mai shekaru 49 zai zama Firaminista na farko a yarjejeniyar da za’a dinga musayar mukamin, yayin da Lapid zai karbi kujerar bayan shekaru 2.

Gabannin kada kuri’ar kawo karshen mulkinsa ne dai tsohon Firaminista Netanyahu ya sha alwashin sake shiri domin karbar jagorancin kasar ta Isra’ila karo na biyu daga hannun ‘yan adawar, tare da bayyana gwamnatinsu a matsayin hatsari ga zaman lafiyar Isra'ila.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.