Isa ga babban shafi
NATO-Amurka

Dole ne NATO ta tunkari China da Rasha- Biden

Shugaban Amurka Joe Biden ya gargadi cewa, dole ne Kungiyar Tsaro ta NATO ta tunkari sabbin kalubalen da ke kunno kai daga China da Rasha, yayin da ya gana da takwarorinsa da zummar sabonta alakar Amurka da kawayenta.

Shugaban Amurka Joe Biden da Sakatare Janar na  NATO Jens Stoltenberg.
Shugaban Amurka Joe Biden da Sakatare Janar na NATO Jens Stoltenberg. REUTERS - POOL
Talla

Shugaba Biden da ya isa shalkwatan NATO da ke birnin Brussels don halartar taron kungiyar da takwarorinsa 29, ya jaddada cewa, wannan kungiya ta NATO na ta matukar muhimmanci ga tsaron Amurka.

Ana kallon ziyarar tasa ta farko a matsayinsa na shugaban kasa zuwa wannan taro da wani yunkuri na kyautata alakar Amurka bayan magabacinsa, wato Donald Trump ya sukurkuta ta.

Kazalika ana kallon wannan ziyara a matsayin wata dama ta sabonta dabarun tunkarar  kalubalen da ke tasowa daga Moscow da Beijing  da kuma nazari kan janyewar NATO cikin gaggawa daga Afghanistan bayan kasar ta shafe tsawon shekaru tana fama da yaki.

Ana sa ran mambobin kasashen na NATO za su amince da wata sanarwa wadda za ta jaddada manufa guda kan janye dakarunsu daga Afghanistan cikin ruwan sanyi, yayin da za su fitar da martanin bai-daya dangane da kutsen da ake yi wa shafukan intanet da kuma barazanar da China ke yi musu.

A zantawarsa da manema labarai, shaugaban NATO, Jens Stoltenberg ya  ce, ba zu da niyar shiga sabon yakin cacar-baka kuma China ba abokiyar gabarsu ba ce a cewarsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.