Isa ga babban shafi
Tattalin arziki-Coronavirus

Tattalin arzikin duniya ya samu tagomashi bayan Korona

Wani rahoto da cibiyar nan da ke bibiyar tattalin arzikin duniya wato HIS ta fitar, ya ce tattalin arzikin duniya ya samu tagomashi fiye da hasashen da aka yi game da farfadowarsa bayan ya shiga mashasshara saboda annobar Korona.

Annobar Korona ta yi wa tattalin arzikin duniya illa
Annobar Korona ta yi wa tattalin arzikin duniya illa REUTERS/Kim Kyung-Hoon
Talla

Cibiyar ta ce, ci gaban da aka samu ba ya rasa nasaba da karfafa gwiwa ga tsarin alluran rigakafin cutar Covid-19 da kasashe suka mayar da hankali a kai, hadi da sassaucin da aka samu daga dokar kulle.

Rahoton wanda aka saba fitarwa a kowanne wata, ya nuna cewa tattalin arzikin duniya ya kai wani muhimmin matsayi a zango na biyu na shekarar 2021, wanda ya zarta na  ma’aunin karfin tattalin arziki na GDP da aka yi a zango na hudun shekarar 2019.

Yankin Asiya ya murmure daga matsin tattalin arziki a karshen shekarar da ta gabata sakamakon karfin tattalin arzikin China.

Masana tattalin arzikin sun kiyasta cewa, ma’aunin karfin tattalin arzikin Amurka ya nuna cewa, an samu ci gaba sosai a kasar a watan Mayu.

Hasashen Cibiyar ya nuna cewa, yankunan Afirka da Gabas ta Tsakiya za su iya farfadowa daga matsin da suka fada daga nan zuwa zango na uku da zai fara a watan Yuli.

Ana sa ran nahiyar Turai da Latin Amurka za su kammala farfadowa nan da karshen shekarar nan.

Sai dai duk da wannan hasashen, Asusun Bada Lamuni na duniya, IMF na ci gaba da jaddada rashin daidaito na murmurewar tattalin arzikin duniya, inda yake ganin cewa, kasashe da dama ba za su samu damar murmurewa ba har zuwa shekarar 2022 ko 2023.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.