Isa ga babban shafi
Amurka-Iraq

Amurka ta kai harin ramuwa kan kungiyoyin da ke samun goyon bayan Iran

Amurka ta ce ta kai hare-hare ta sama kan dakaru da ke samun goyon bayan Iran a kusa da kan iyakar Iraki da Syria domin mayar da martani ga hare-hare da jirage marasa matuka suka kai kan dakarunta a Iraki. Wani mai magana da yawun ma'aikatar tsaron Pentagon ya ce an kai harin ne kan wasu wurare uku da ake ajiyar makamai a yankin.

Shugaban Amurka Joe Biden.
Shugaban Amurka Joe Biden. AP - Evan Vucci
Talla

Kimanin sojin Amurka 2500 ke Iraki a zaman wani bangare na kawancen kasashen duniya da ke tallafawa jami’an tsaron cikin gida a yakin da su ke yi da kungiyar IS.

Sanarwar ta ruwaito shugaba Joe Biden na bayyanawa karara cewa Amurka za ta ci gaba da baiwa dakarunta kariya da ke yankin.

Tuni dai kungiyar PMF ta tabbatar da mutuwar dakarunta hudu a farmakin, yayinda ta sha alwashin daukar fansa.

Rahotanni sun ce akwai akalla hare-haren jirage marasa matuka sau biyar da aka kaddamar a wuraren ajiyar makaman daga watan Afrilu, baya ga yawan harin rokoki da ake samu a yankin.

Tuni dai gwamnatin Iraqi ta yi tir da wannan hari ta na bayyana hakan a matsayin barazana ga bangaren tsaron kasar

Amurka dai ta ce cibiyoyin da aka kai harin sun kasance a wurare biyu da ke Syria da kuma daya a cikin Iraki, kuma kungiyoyin da ke samun goyon bayan Iran sun yi amfani da shi, ciki har da Kataib Hezbollah da Amurkan ta ayyana a matsayin kungiyar ta’addanci ta duniya tun a 2009, kuma ta zarge ta da kai hare-hare da dama kan sojojin Amurka a Iraki a shekarun baya-bayan nan

Kafofin yada labaran Syria sun ruwaito cewa an kashe wani yaro a kusa da iyakar Syria da Iraki, kuma sun zargi Amurka da neman yin kafar ungulu ga kokarin inganta zaman lafiya a yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.