Isa ga babban shafi
ITALIA-KORONA

Ba zamu karbi allurar rigakafi ba - Likitocin Italia

Wasu ma’aikatan lafiya 300 a kasar Italia sun kai gwamnatin kasar kotu inda suke kalubalantar ta kan tilasta musu karbar allurar rigakafin cutar korona ba tare da son ran su ba.

Firaministan Italia Mario Draghi
Firaministan Italia Mario Draghi AP - Riccardo Antimiani
Talla

Ana saran kotu ta fara sauraron wannan kara da ma’aikatan lafiyar da suka fito daga yankin arewacin Italia suka gabatar a ranar 14 ga watan nan na Yuli.

Masanin shari’a Daniele Granara da ya taimaka wajen rubuta takardar karar da aka gabatar a kotu ke yace batun ba wai na masu yaki da allurar rigakafin bane, sai dai batu ne na dimokiradiya inda kowa ke da hurumin zabin abinda yake so.

Granara wanda yanzu haka ke tsayawa tarin ma’aikatan lafiya da aka dakatar daga ayyukan su saboda kin yarda su karbi allurar rigakafin cutar na sahun gaba wajen gurfanar da gwamnati a kotu.

Alamun cutar korona
Alamun cutar korona © 网络照片 Getty Images/iStockphoto - ismagilov

A watan Afrilun da ta gabata gwamnatin Italia ta amince da wata doka wadda ta ce ya zama dole duk wani ma’aikacin kula da lafiya da suka hada da likitoci da masu harkar bada magunguna su karbi allurar rigakafin cutar korona domin kare lafiyar su da ta mutanen da suke dubawa.

A karkashin shirin gwamnatin kasar masu yawan shekaru da masu kula da marasa lafiya da kuma malaman makarantu aka fara gabatarwa da allurar rigakafin a kasar Italia.

Ya zuwa wannan lokaci an baiwa jama’a allurar rigakafi kusan miliyan 53 a fadin kasar, kuma akalla yan kasar miliyan 19 da rabi sun karbi maganin sau biyu.

Alkaluma sun bayyana cewar ma’aikatan lafiya dubu 45,750 daga cikin miliyan guda da dubu 900 sun ki karbar allurar ko da sau guda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.