Isa ga babban shafi
OPEC - Man Fetur

Takaddama tsakanin Saudiya da Daular Larabawa ta tilasta dage taron OPEC

Cacar bakan da ta barke tsakanin Saudiya Hadaddiyar Daular Larabawa ta tilasta dage taron da aka fara a ranar Litinin na kungiyar kasashe masu arzikin man fetur ta OPEC da kuma kawayenta kan shirin daukar matakin rage hauhawar farashin danyen mai a duniya.

Kasashen OPEC sun gaza cigaba da taro saboda takaddama tsakanin Daular Larabawa da Saudiya.
Kasashen OPEC sun gaza cigaba da taro saboda takaddama tsakanin Daular Larabawa da Saudiya. © REUTERS - DADO RUVIC
Talla

Takaddamar ta samo sali ne bayan da Hadaddiyar Daular Larabawa ta ki amincewa da shawarar sauran kasashe 22 masu arzikin man fetur na ciki da wajen kungiyar OPEC kan neman kara yawan gangunan danyen man da suke hakowa domin daidaita farashinsa dake cigaba da dagawa yanzu haka bayan farfadowa da shakar tasirin annobar Korona.                   

Tun cikin watan Mayun da ya gabata kasashen 23 masu arzikin danyen mai na ciki da wajen kungiyar OPEC ke kara yawan danyen man da suke hakowa da kadan kadan, bayan zaftare shi da suka yi a shekarar bara, saboda mummunar fadowar da farashinsa yayi a dalilin barkewar cutar Korona.

Kudirin bayan bayan nan da kasar Daular Larabawa ta hau kujerar naki akai shi ne na kara yawan danyen man da kungiyar OPEC da kawayenta ke hakowa duk rana da adadin ganguna dubu 400 duk wata daga Agustan dake tafe har zuwa karshen shekarar nan da muke, adadin da zai kai ganga miliyan 2 kenan a kowace rana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.