Isa ga babban shafi
Amurka-Iraqi

Amurka da Iraqi sun bude sabon babin hulda

Shugaba Joe Biden ya ayyana cewa alakar Amurka da Iraqi za ta shiga wani sabon salo, yayin da sojojin Amurkan ke ficewa daga Iraqin bayan ayyukan wanzar da zaman lafiya da suka dauki tsawon shekaru suna yi.

Shugaban Amurka Joe Biden, na musafaha da Firaministan Iraqi Mustafa al-Kadhimi.
Shugaban Amurka Joe Biden, na musafaha da Firaministan Iraqi Mustafa al-Kadhimi. AP - Susan Walsh
Talla

Mista Biden na bayyana hakan ne a tattaunawarsa da Firaministan Iraqi, Mustafa al-Kadhemi a fadar White House.

Duk da barazanar dawowar kungiyar IS mai da’awar jihadi, da kuma tasirin Iran a birnin Bagadaza, shugaba Biden ya jaddada cewa Amurka za ta ci gaba da bai wa Iraqi goyon baya a bangaren tsaro.

Mista Biden ya ci gaba da cewa dakarun Amurka za su ci gaba da tallafawa da kuma bai wa takwarorinsu na Iraqi horo, musamman ma yadda za su tunkari mayakan ISIS da ke barazanar sake mamaye kasar.

Shugaban na Amurka ya kuma jaddada goyon bayan kasarsa ga zaben a watan Oktoba a Iraqi, yana mai cewa fadar White House na aiki kafada da kafada da kasar da Majalisar Hadin Kan kasashen Larabawa da Majalisar Dinkin Duniya don tabbatar da cewa an gudanar da sahihin zabe.

Gwamnatin Iraqi ta sanar da fatattakar kungiyar IS a karshen shekarar 2017, amma masu tsattsauran ra'ayin sun kara kaimi inda har yanzu suke ci gaba da kai hare-haren kunan bakin wake akai-akai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.