Isa ga babban shafi
Coronavirus

Za a rika bai wa Amurkawa kudi don su yi rigakafin Korona

Gwamnatocin kasashen duniya sun dukufa wajen magance yaduwar sabon nau’in cutar Covid-19 da ake kira Delta, inda shugaban Amurka Joe Biden ya umarci hukumomin kasar da su bada ladar kudi domin shawo kan wadanda suka ki karbar allurar rigakafin annobar.

Shugaban Amurka Joe Biden
Shugaban Amurka Joe Biden AP - Susan Walsh
Talla

Ita ma Isra’ila ta bada umarnin kaddamar da shirin rigakafin cutar a karo na uku ga al’ummar kasar musamman wadanda suka haure shekaru 60, a daidai lokacin da Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta yi gargadin cewa, sabon nau’in na Korona ka iya haddasa sake barkewar  annobar a karo na hudu musamman a yankin gabashin Mediterranean.

Kasashen na gabashin Mediterranean kama daga Morocco har zuwa can bangaren Pakistan, na fuskantar barazanar sake barkewar cutar, lura da cewa, kashi 5.5 na daukacin al’ummar yankin kadai aka yi wa rigakafi cikakke.

A yayin gabatar da jawabinsa game da dakile wannan annoba, shugaba Biden na Amurka ya ce, mutane na mutuwa kuma za su ci gaba da mutuwa duk da cewa, bai kamata su mutu ba koda kuwa ba a yi musu rigakafi ba.

Shugaban ya ce, za a umarci daukacin ma’aikatan gwamnatin tarayyar Amurka da su nuna shedar rigakafinsu, sannan dole ne ga wadanda ba su da rigakafin su rike tamke fuskokinsu da takunkumi a wuraren aiki, baya ga gwajin Covid-19 a-kai a-kai da za su rika yi.

Biden ya kuma umarci gwamnatocin jihohi da na kananan hukumomi da su bada ladar Dala 100 don shawo kan mutane har su yi wannan rigakafi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.