Isa ga babban shafi
SAUYA-SHEKA

PSG ta fara tattaunawa da Lionel Messi

Kungiyar kwallon kafar Paris St-Germain dake kasar Faransa ta fara tattaunawa da wakilin ‘dan wasan Argentina Lionel Messi bayan raba hannun rigar da yayi da kungiyar Barcelona a ranar alhamis.

Lionel Messi na ban kwana da magoya bayan Barcelona
Lionel Messi na ban kwana da magoya bayan Barcelona Josep LAGO AFP/File
Talla

Rahotanni sun ce bangarorin biyu sun yi tattaunawar farko a ranar alhamis kuma yau asabar ake saran su ci gaba da ganawa domin amincewa da kwangilar da zata kaiga Messi ya koma Paris domin yiwa PSG wasa tare da tsohon abokin tafiyar sa Neymar Jnr.

kafar yada labaran RMC Sport ta ruwaito cewar Messi ya bayyana aniyar sa ta komawa PSG yayin da ake ci gaba da tattaunawa domin amincewa da kwangilar shekaru 2.

Kungiyar Barcelona ta sanar da cewar ba zata iya mutunta yarjejeniyar da ta kulla da Messi ba saboda rashin kudi da kuma dokar kula da gasar La Liga da ta kayyade irin kudaden da ya dace kowacce kungiya ta kashe, abinda ya kawo karshen zaman sa na shekaru sama da 20 a kungiyar.

Shugaban Barcelona Joan Laporta yace ci gaba da rike Messi a kungiyar su zai haifarwa kungiyar asarar da zata kai na shekaru 50 saboda dokar gudanar da wasan kasar.

Messi ya bugawa wasannin sama da 700 ya kuma jefa kwallaye 672 da lashe gasar La Liga sau 10 da kofin zakarun Turai sau 4 da Kofin Kalubale sau 7, yayin da sau 6 yana lashe kyautar ‘dan wasan da yafi kowa a duniya.

Barcelona tace gobe lahadi Messi zai halarci taron ganawa da manema labarai inda ake saran yayi ban kwana da magoya bayan kungiyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.