Isa ga babban shafi
China - WHO

China ta yi watsi da bukatar WHO kan karin binciken asalin Korona

China ta yi watsi da kiran da Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta yi mata a wannan Juma’a, dangane da sake sabon bincike kan asalin annobar Korona, inda ta ce matsayin ta shi ne fifita Kimiyya, sabanin amfani da Siyasa wajen gano yadda cutar ta samo asali.

Hoton taswirar duniya zagaye da kwayoyin cutar Korona.
Hoton taswirar duniya zagaye da kwayoyin cutar Korona. © 网络照片 Getty Images/iStockphoto - ismagilov
Talla

Yanzu haka dai matsin lamba na karuwa kan gwamnatin China kan bukatar baiwa tawagar kwararru na kasa da kasa damar gudanar da sabon bincike don gano asalin Korona da yadda annobar ta barke, wadda kawo yanzu ta kashe mutane sama da miliyan hudu tare da gurgunta tattalin arzikin duniya tun bayan bullarta a birnin Wuhan na kasar ta China a Disamban shekarar 2019.

A watan Janairun shekarar nan da ya gabata, wata tawagar kwararrun kasa da kasa ta hukumar lafiya ta duniya ta ziyarci birnin Wuhan domin tattara kashin farko na rahoton yadda cutar Korona ta barke, said ai sun gaza cimma matsaya da takwarorinsu na kasar China kan bayanan yadda annobar ta samo asali.

Shugaban hukumar lafiya ta duniya WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus.
Shugaban hukumar lafiya ta duniya WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus. © KEYSTONE/MARTIAL TREZZINI sda-ats

A ranar Alhamis ne dai hukumar WHO ta bukaci China da ta mika mata wasu bayanan binciken da kwararrun kasar suka tattara na mutanen suka fara kamuwa da Korona, domin farfado da bincikenta kan asalin cutar.

Sai dai Chinar ta mayar da martani cikin kakkausan harshe, inda ta nanata matsayinta na cewa binciken farko da kwararrun hukumar lafiyar ta duniya suka gudanar a watan Janairu ya isa, zalika  kiraye-kirayen da ake mata na neman karin bayanai kan annobar ta Korona siyasa ce kawai a maimakon niyyar da ta kafu kan binciken kimiyya zalla.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.