ISIS na shirin kai hari a filin jiragen sama na Kabul
Kasashen Amurka da Birtaniya da Australia na gargadin jama’arsu da ke Afghanistan game da yin balaguro zuwa filin jiragen sama na birnin Kabul bayan wasu bayanan sirri sun nuna cewa, ‘yan ta’adda na shirin kaddamar da farmaki kan mai uwa da wabi.
Wallafawa ranar:
Tuni Amurka da Australia da Birtaniya suka shaida wa ‘yan kasashensu cewa, su gaggauta ficewa daga harabar filin jiragen saman na birnin Kabul.
Tun da farko shugaban Amurka Joe Biden ne ya yi gargadin cewa, akwai barazanar wasu tsageru masu alaka da mayakan ISIS za su kai harin.
Shi ma Ministan Kula da Ayyukan Sojojin Birtaniya, James Heappey ya ce, a halin yanzu, akwai bayanan sirri masu inganci game da yiwuwar kaddamar da farmakin nan kusa, yana mai bukatar jama’ar da ke son ficewa da su dakatar da halartar filin jiragen sama na Kabul a yanzu.
Kodayake Heappey ya ce, za su yi iya bakin kokarinsu domin tabbatar da tsaron lafiyar jama’ar da ke dako a filin jiragen saman, amma za su sauya shawara da zaran sun samu sabbin rahotanni a cewarsa.
Tun da farko dai, mayakan Taliban sun yi alkawarin samar da tsaro a harabar filin jiragen saman, amma dai kasashen yammacin duniya ba za su yi sakaci da rahoton yiwawur kaddamar da farmakin ba daga ISIS kamar yadda wani jakada na kungiyar NATO ya shaida wa Reuters.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da aka kwashe akalla mutane dubu 80 daga Afghanistan don guje wa zalincin Taliban, kuma har yanzu akwai sauran dubbai da ke jiran ficewa daga kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu