Isa ga babban shafi
RIKICIN-AFGHANISTAN

Mutane 13 sun mutu sakamakon harin ta'addanci a Kabul

Wani harin bama bamai a wajen tashar jiragen saman Kabul dake Afghanistan ya girgiza birnin sa’oi bayan kasashen yammacin duniya sun yi gargadi samun kai harin ta’addanci a filin jirgin dake dauke da dubban mutanen dake kokarin ficewa daga kasar.

Shugabannin Taliban
Shugabannin Taliban AFP - -
Talla

Mai magana da yawun ma’aikatar tsaron Amurka John Kirby ya tabbatar da aukuwar fashewar, sai dai ya zuwa wannan lokaci ba’a iya tantance irin ta’addin da aka samu ba da kuma yawan mutanen da suka jikkata, amma wani jami’in kungiyar Taliban Zabihullah Mujahid yace mutanen da suka mutu zasu kai tsakanin 13 zuwa 20, yayin da wadanda suka jikkata sun kai 50 cikin su harda sojojin Amurka.

Shugaban Amurka John Biden ya bayyana fargabar samun irin wannan harin daga Yan ta’addan ISIS sakamakon yawan mutanen da ake da su a tashar jiragen dake kokarin ficewa daga kasar.

Masu kokarin barin Afghanistan
Masu kokarin barin Afghanistan AFP - WAKIL KOHSAR

Wannan ya sa kasashen yammacin duniya suka gargadi al’ummar su dake Afghanistan da su kaucewa zuwa tashar jiragen har sai an bukace su da yin haka domin kaucewa irin wannan harin.

Cikin wadanda suka gabatar da irin wannan gargadi harda Firaministan Belgium Alexander De Croo da hukumomin Amurka da Birtaniya.

Ya zuwa yanzu akalla mutane dubu 95 daga cikin ‘Yan kasashen waje da ‘Yan kasar Afghanistan suka yi nasarar barin Afghanistan tun bayan fara jigilar su ranar 15 ga watan Agusta sakamakon karbe iko da kasar da kungiyar Taliban tayi.

Wannan ya sa dubban mutane suka yiwa tashar jiragen Kabul cincirindo domin ganin sun fice dan kaucewa mulkin kungiyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.