Isa ga babban shafi
HARIN-TA'ADDANCI

Kwamitin Sulhu ya bukaci hukunta wadanda suka kai harin Afghanistan

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya bukaci kasashen duniya da suyi aiki tare wajen ganin an zakulo wadanda suka kai harin ta’addanci birnin Kabul dake Afghanistan domin hukunta su.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres Javier Soriano AFP/Archivos
Talla

Sanarwar da wakilan kwamitin 15 suka rattabawa hannu ta jaddada muhimmancin hukunta wadanda suka shirya da kuma kai harin tare da wadanda suka dauki nauyin sa.

Kwamitin ya bukaci daukacin kasashen duniya da suyi aiki tare da dokokin da aka tanada tare da kudirorin Kwamitin sulhun domin samun nasara akai.

Wani daga cikin wadanda harin Kabul ya ritsa da shi
Wani daga cikin wadanda harin Kabul ya ritsa da shi Wakil KOHSAR AFP

Akalla mutane kusan 100 suka mutu sakamakon kazamin harin cikin su harda sojojin Amurka 12, abinda ya sa shugaba Joe Biden ya alwashin farautar wadanda ke da hannu a harin domin hukunta su.

Hukumar kula da ‘Yan gudun hijira ta Majalisar tace ana iya samun akalla mutane sama da dubu 500 da zasu bar Afghanistan nan da karshen wannan shekara sakamakon karbe iko da kungiyar Taliban tayi, saboda haka ya zama wajibi a gare ta da ta shirya karbar su.

Mataimakiyar kwamishiniyar kula da Yan gudun hijirar Kelly Clements ta bayyana haka sakamakon yadda Yan kasar Afghanistan ke kwarara suna barin kasar.

Yanzu haka kasashen yammacin duniya da dama na ci gaba da kwashe ‘yan kasashen su da wasu Yan Afghanistan ta hanyar jiragen sama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.