Sabon gwajin maganin zazzabin malaria ya yi tasirin kashi 70 a Afirka
Wani sabon tsari na yin amfani da magungunan da ake da su don samar da kariya daga zazzabin cizon sauro na Malaria ya nuna alamun rage radadin cutar a tsakanin jarirai da kaso 70 a nahiyar Afrika kudu da sahara, kamar yadda wani bincike ya nuna.
Wallafawa ranar:
Wannn sakamakom mai mahimmanci da aka wallafa a mujalar kiwon lafiya ta New England Journal of Medicine ya zo ne bayan da aka hada aka hada maganin zazzabin cizon sauro da na rigakafin zazzabin gabanin lokacin damuna.
Zazabin cizon sauro dai na kashe fiye da mutane dubu 400 a duk shekara, kuma akasarin wadanda yake kashewa yara ne ‘yan kasa da shekaru 5.
Babban jami’i na wannan bincike Brian Greenwood na kwalejin kiwon lafiya ta Landn ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa cewa tawagarsa na tattaunawa da hukumar Lafiya ta Duniya a kan sanya shawarwarin binciken a kundinta.
Binciken da aka yi a da can ya nuna cewa kariya da rigakafin zazzabin cizon sauro ke bayarwa ta tabarbare, inda take tasirin kashi 30 a cikin shekaru 3 zuwa 4.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu