Isa ga babban shafi
Afghanistan-Amurka

Taliban ta yi bikin ficewar Amurka daga Afghanistan

Mayakan Taliban sun yi bikin murnar karbe iko da gwamnatin Afghanistan baki daya bayan Amurka ta kammala ficewa daga kasar a yau Talata, inda suka yi ta harbe-haren bindiga a sararin samaniya.

Jagororin mayakan Taliban a filin jiragen sama na birnin Kabul.
Jagororin mayakan Taliban a filin jiragen sama na birnin Kabul. WAKIL KOHSAR AFP
Talla

A hukumance, Amurka ta kawo karshen yaki mafi dadewa da ta yi tarihi, domin kuwa ta shafe kimanin shekaru 20 tana fafatawa da ‘yan ta’adda a Afghanistan.

Dakarun Amurka sun fice daga filin jiragen sama na birnin Kabul, inda suka shafe tsawon kwanaki suna sanya ido kan kwashe jama’ar da ke son ficewa daga Afghanistan.

Sama da mutane dubu 123 ne aka kwashe daga kasar ta Afghanistan domin tsoron mulkin zalinci na Taliban.

Jim kadan da ficewar sojojin Amurka, mayakan na Taliban sun mamaye harabar filin jiragen sama na birnin Kabul tare da harbe-harben bindigogi domin nuna murna.

A yayin jawabinsa, mai magana da yawun Taliban, Zabihullah Mujahid ya shaida wa manema labarai cewa, wannan nasarar da suka samu ta Afghanistan ce.

Kazalika ya ce, wannan nasarar wata mauniya ce da ke matsayin darasi ga manyan kasashe masu mamayar kananan kasashe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.