Isa ga babban shafi
Gurbatar Muhalli

Yawan sharar roba ka iya zarta adadin kifayen teku nan da 2050 - Kwararru

Kungiyar Tarayyar Turai EU ta goyi bayan kiraye-kirayen kulla yarjejeniya ta kasa da kasa domin rage gurbatar muhallin tudu da na ruwa sanadin tulin sharar kayayyakin da suka kunshi dangogin roba da na leda.

Yadda tarin sharar robobi da ledoji ta mamaye gabar teku a Manila babban birnin kasar Philippines.
Yadda tarin sharar robobi da ledoji ta mamaye gabar teku a Manila babban birnin kasar Philippines. REUTERS/Erik De Castro/Files
Talla

EU ta bayyana matsayin nata ne a yayin taro da Majalisar Dinkin Duniya ta shirya a birnin Geneva kan gurbatar muhalli.

Wani jami'in gwamnatin Jamus ya ce tuni kasashe 75 suka goyi bayan daftarin kudurin neman kulla. yarjejeniyar daukar matakan bai daya tsakaninsu don magance matsalar da gurbatar muhallin dan Adam da sharar roba.

Ministan Faransa mai kula da ayyukan sa ido kan rayuwar halittu da muhallinsu Berangere Abba, ya ce muddin duniya ta gaza daukar matakin da ya dace, to fa babu shakkah yawan sharar roba da ledoji a cikin teku zai zarta na kifaye nan da shekarar 2050.

Hoton da aka ɗauka a ranar 2 ga Yuni, 2018 da ke nuna tsuntsu tsaye a bakin teku cike da sharar robobi a Hann Bay da ke birnin Dakar.
Hoton da aka ɗauka a ranar 2 ga Yuni, 2018 da ke nuna tsuntsu tsaye a bakin teku cike da sharar robobi a Hann Bay da ke birnin Dakar. © Seyllou/AFP

Shirin kula da Muhalli na Majalisar Dinkin Duniya, wanda ke daukar nauyin taron na birnin Geneva, yayi gargadin cewa yanzu haka duniya tana "nutsewa cikin gurbataccen muhallin da sharar robobi da ledoji ke yiwa illa, sakamakon yadda a duk shekara ake tara sharar da yawanta ya kai kusan ton miliyan 300.

Binciken kwararru ya nuna cewa, tun daga shekarun 1950 zuwa yanzu, an tara kusan ton biliyan 8 da miliyan 300 na sharar robobi da ledoji a sassan duniya, wanda kuma kusan kashi 60 na sharar an zubar da ita ne akan tudu.

Ragowar kashi 40 kuma na miliyoyin ton din sharar robobin na karewa a cikin tekuna, lamarin da ya haifar da mutuwar tsuntsayen ruwa fiye da miliyan daya, da kuma mutuwar wasu dabbobin masu shayarwa akalla dubu 100 kowace shekara a teku.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.