Isa ga babban shafi
Sauyin Yanayi

Dumamar yanayi na sauya wa tsuntsaye fasalin halittarsu

Wani sabon rahoton masana na nuna cewa, matsalar dumamar yanayi da ake fama da ita a duniya, na shafar hatta dabbobin da ke rayuwa a sararin samaniya, inda matsalar ke sauya musu zubin  halitta.

Wasu tsuntsaye na shawagi a sararin samaniya
Wasu tsuntsaye na shawagi a sararin samaniya AP - David Goldman
Talla

Rahoton masanan na cewa, fasalin jikin tsuntsaye kamar akukuturu na Australia da zomaye na Turai na sauyawa saboda tasirin matsalar dumamar yanayi.

Sara Ryding mai bincike a Jamiar Deakin ta kasar Australia wadda ta jagoranci binciken dabbobin, na ganin lokaci ya yi da za a bai wa dabbobi kulawa domin su tafi daidai da zamani.

Wannan binciken da aka wallafa a wannan Talatar, ya yi nazarin wasu nazarce-nazarce na baya game da sauyin halittun dabbobi a dalilin sauyin yanayi a duniya, inda aka fara gano sauyin a cikin tsuntsaye.

Binciken ya karas da cewa, ana samun kari wajen girman aku na kasar Australia da kashi 4 cikin 100 bisa yadda yake a shekara ta 1871.

Haka ma an gano cewa, sauran tsuntsaye na wasu kasashen Turai sun kara girman jiki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.