Isa ga babban shafi

Yan taliban sun karbe kusan dalar Amurka milyan 12 da wasu kadarori

Babban bankin Afghanistan ya bayyana cewar kungiyar Taliban ta yi nasarar karbe tarin kudade da yawansu ya kai dalar Amurka miliyan 12 da kuma tarin gwalagwalai a gidajen tsoffin Jami’an gwamnatin kasar.

Wasu daga cikin masu hadadar kudi a Afghanistan
Wasu daga cikin masu hadadar kudi a Afghanistan Wakil KOHSAR AFP/File
Talla

A kasar ta Afghanistan an dauki tsawon lokaci ba a biya ma’aikatan kasar albashi, abinda ya sanya su gwagwarmayar neman yadda za’a magance wannan al'amari.

Hatta wadanda keda kudi a bankuna suma sun kasance cikin halin kaka nikayi saboda adadin kudin da za’a cira a rana bai wuce $200 ba.

Al'umar kasar Afghanistan
Al'umar kasar Afghanistan REUTERS - STRINGER

Kuma yayin da batun sakonnin kudi daga kasashen waje ya fara shiga kasar kostomomin bankuna na dirar mikiya a Bankuna inda suke cin karo da rashin wadatattun kudi da za a basu.

Bisa wannan dalili ne ya sanya Bankuna suka yi kira ga al’umar kasar da su rika cirar kudin cikin gida ba na kasashen waje ba.

Wasu yan kasar ta Afghanistan cikin bankunan kasar
Wasu yan kasar ta Afghanistan cikin bankunan kasar Wakil KOHSAR AFP/File

Babban Bankin ya sanar da cewar Mayakan Taliban sun mika musu Dalar Amurka har miliyan 12.3 zunzurutu da kuma gwalagwalaia hannun su.

Inda babban Bankin yace an samo kudaden ne daga hannun tsoffin manyan Jami’an gwamnatin kasar ta Afghanistan.

 Amir khan Muttaqi Ministan harakokin wajen Afghanistan
Amir khan Muttaqi Ministan harakokin wajen Afghanistan AFP - HOSHANG HASHIMI

Kudaden da ya zuwa yanzu ba’a san dalilin da ya sanya manyan tsoffin gwamnatin kasar suka boye su ba

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.