Isa ga babban shafi

Mutane kusan milyan biyu ke mutuwa kowacce shekara sakamakon haduran wurin aiki

Majalisar Dinkin Duniya tace akalla mutane kusan milyan biyu ke mutuwa kowacce shekara sakamakon hadura da raunukan da suke samu a wuraren aiki, inda take gargadin cewar annobar korona na iya fadada illar da ake gani.

Wasu daga cikin ma'aikata a wani filin kwallon kafa
Wasu daga cikin ma'aikata a wani filin kwallon kafa Karim ABOU MERHI AFP/Archives
Talla

Wannan nazari na hadin gwiwa tsakanin hukumar lafiya ta duniya da hukumar kwadago a kan cutuka da raunuka da ke addabar ma’aikata ya mayar da hankli ne a kan al’amuran da suka gudana a tsakanin shekara ta 2000 zuwa 2016, kuma bai kunshi sauye sauye da aka samu a yanayin aiki da annobar Covid 19 ta taho da shi ba.

Wasu daga ma'aikata a kasashen Duniya
Wasu daga ma'aikata a kasashen Duniya AFP - MUNIR UZ ZAMAN

A shakarar  2016, mutuwar mutane  miliyan 1 da dubu dari 9 ne aka danganta da raunuka ko cutuka da suka samu a wuraren ayyukansu, wato ya karu daga miliyan 1 da dubu dari 7 da yake a farko wannan karnin.

 

Rahoton da hukumomin 2 suka fitar ya yi nuni da cewa shafe tsawon lokaci ko aikin sa’o’i 55 a mako, ko fiye a wajen aiki ne hatsari mafi muni, kuma shine ummul’aba’isin mjutuwar mutane dubu dari 7 da 50 a shekarar 2016.

Ma'aikata a Bama
Ma'aikata a Bama © REUTERS/Soe Zeya Tun

Gaba daya dai, binciken ya yi nazari ne a kan haddura 19   da ma’aikata ke fuskanta a wuraren ayyukansu da suka hada da shakar sinadarai masu hadari kamar na carcinogens da kuma zama wuri daya na tsawon lokaci da sauransu.

A wata sanarwa, shugaban hukuma lafiya ta duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce abin takaici ne ganin yadda mutane da dama ke mutuwa a yayin gudanar da ayyukansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.