Isa ga babban shafi
Tattalin Arziki

Farashin mai ya haura sama da dala 80 a karon farko cikin shekaru uku

A karon farko cikin shekaru 3, farashin danyen man fetur ya haura sama da dala 80 kan kowace ganga.

Gangunan danyen man fetur a gefe takardar kudin dalar Amurka (hoto domin misali)
Gangunan danyen man fetur a gefe takardar kudin dalar Amurka (hoto domin misali) © REUTERS/Dado Ruvic/Illustration
Talla

Tun a ranar Talatar da ata gabata farashin man ya kai dala 80.69, darajar da rabon da gangarsa ta samu tun watan Oktoban shekarar 2018.

Bayanai dai sun ce farashin man ya yi ta hauhawa ne tsawon kwanaki bakwai, a yayin da kuma manazarta ke ganin cewa darajar ta sa, za ta ci gaba da karuwa sakamakon yadda bukatar danyen man ke karuwa, la’akari da matakan da kasashe masu arzikinsa ke dauka na takaita adadin wanda suke hakowa a kowace rana domin farfado da kimarsa.

Farashin man fetur dai ya fadi warwas a farkon barkewar annobar Korona, inda a watan Afrilu na shekarar 2020, hada-hadar cinikinsa ta tsaya cik, karon farko a tarihi, biyo bayan matakan kullen da hukumomin kasashe suka dauka akan al’ummominsu, a daidai lokacin da su kuma kasashe masu arzikin danyen man na kungiyar OPEC da kawayensu basu fasa hako shi ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.