Isa ga babban shafi
Amurka-Corona

Corona ta kashe tsohon sakataren wajen Amurka Collin Powell

Tsohon sakataren harkokin wajen Amurka Janar Collin Powell da ya taka rawa wajen mamaye kasar Iraqi, kuma baki na farko da ya rike wannan mukamin, ya rasu sakamakon cutar korona ya na da shekaru 84 a duniya.

Colin Powell tsohon sakataren wajen Amurka da ya taka rawa wajen mamayar Iraqi.
Colin Powell tsohon sakataren wajen Amurka da ya taka rawa wajen mamayar Iraqi. AP - Michael Caulfield
Talla

Iyalan Collin Powell ne suka bayyana rasuwar yau, inda suka bayyana shi a matsayin Uba da Kaka na gari, wanda ya bada gudumawa wajen kare Amurka.

Tsohon Babban hafsan sojin Amurkan wanda yayi aiki da shugaban kasa guda 4, ya nesanta kann sa daga harkokin siyasa, abinda ya sa mutane suke girmama shi.

Tsohon shugaban kasa George W. Bush ya bayyana Powell a matsayin gwarzon Amurka, abin misali a kasar da kuma wanda za’a ci gaba da bada tarihin sa, lokacin da ya gabatar da sunan sa domin zama Sakataren harkokin waje a shekara ta 2000.

A shekarar 2003, Janar Powell ya shaidawa Majalisar Dinkin Duniya takaicin sa na mamaye Iraqi wadda aka zarga da mallakar makamin nukiliya.

A hirar da yayi da tashar ABC News Janar Powell ya bayyana mamayar Iraqi a matsayin tabon da zai ci gaba da rayuwa da shi har mutuwar sa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.