Isa ga babban shafi
WHO-Coronavirus

Ana bukatar sama da dala biliyan 23 don yaki da annobar Korona-WHO

Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta ce ana bukatar Dala biliyan 23 da miliyan 400 nan da farkon shekara mai kamawa don yaki da cutar Covid-19.

Shugabann hukumar lafiya ta duniya Tedros Adhanom Gabreyesus.
Shugabann hukumar lafiya ta duniya Tedros Adhanom Gabreyesus. REUTERS - DENIS BALIBOUSE
Talla

A cewar hukumar, har yanzu akwai bukatar makudan kudade don tallafa wa wasu kasashen da alluran da kuma tabbatar da cewa sun isa ga kasashe matalauta.

Hukumar ta ce, a yadda cutar ke nuna alamu, nan da kowane lokaci zata iya tsananta a kasashe , don haka akwai bukatar tara kudaden don samar da na’urorin taimaka wa numfashi da sauran kayayyakin aiki isassu, a fadin duniya.

Shugaban hukumar, Tedros Adhanom Ghebreyesus ya fito fili karara inda ya bayana wa kasashe masu karfin arzikin na duniya 20, cewa lokaci yayi da za su yi gamayyar taimakawa kasashe marasa karfi

Nahiyar Afrika dai ita ce a baya, la’akari da cewa zuwa yanzu, kaso 8 na al’ummar nahiyar ne kawai suka karbi rigakafin farko, a cewar Cyril Ramaphosa Shugaban Afrika ta kudu. A yayin da kididdiga ta nuna kasashe 5 na Afrika daga cikin kasashe 54 ne suka cimma hasashen hukumar lafiyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.