Isa ga babban shafi
Amurka - EU

Amurka da EU sun janye harajin karafa da dalma dake tsakaninsu

Shugaban Amurka Joe Biden da Shugabar Hukumar Kungiyar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen sun yi jinjina ga abin da suka kira ‘sabon babi’ a huldarsu bayan wata yarjejeniya da suka cimma a birnin Rome domin janye kudaden harajin karafa da dalma.

Shugaban Amurka Joe Biden tare da shugabar Hukumar gudanarwar EU Ursula von der Leyen, lokacin taron G20 a Rome, 31/10/21.
Shugaban Amurka Joe Biden tare da shugabar Hukumar gudanarwar EU Ursula von der Leyen, lokacin taron G20 a Rome, 31/10/21. Brendan SMIALOWSKI AFP
Talla

Hukumomin Amurka sun ce wannan sabuwar yarjejeniya da aka cimma, ba kawai za ta janye kudin harajin ba ne wanda tsohon shugaba Donald Trump ya lafta, za ta samar da hatta karafa mafi inganci kuma cikin farashi mai rahusa, yayin da za a inganta hanyoyin safarar hajar a kasashen duniya.

A yayin gabatar da taron menema labarai a birnin na Rome, shugaba Biden ya ce, wannan sabuwar hulda a tsakaninsu da kungiyar Tarayyar Turai za ta amfanar da al’ummomin bangarorin biyu a yanzu da kuma shekaru masu zuwa nan gaba.

Ita ma a nata jawabin, shugabar Hukumar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen ta ce, a yanzu dai sun maido da aminci da kuma musayar bayanai a tsakaninsu da Amurka.

A ranar Asabar din da ta gabata ne, Amurka da Kungiyar EU suka cimma yarjejeniyar ta janye kudin harajin , lamarin da ya warware rikicin da ya sukurkuta alakar kasuwanci a tsakaninsu wanda ya samo asali a zamanin mulkin Trump.

A shekarar 2018 ne, Mista Trump ya lafta harajin kashi 25 kan karafa da kuma kashi 10 kan dalmar da ake shigowa da su cikin Amurka daga kasashen duniya da dama da suka hada da nahiyar Turai, inda a wancan lokacin ya yi ikirarin cewa, ya dauki matakin ne a dalilai na tsaron kasa, ikirarin da tuni manazarta suka yi watsi da shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.