Isa ga babban shafi
Mali-Rasha

Za mu ci gaba da aikin soji da Mali - Rasha

Gwamnatin Rasha ta sha alwashin ci gaba da hadin gwiwar soji da kasar Mali da kuma kare martabar yankin Sahel, yayin da ta musanta alaka da wasu 'yan kwangilar soja da ake danganta su da kasarta.

Shugaban Rasha Vladimir Putin
Shugaban Rasha Vladimir Putin Alexey NIKOLSKY SPUTNIK/AFP
Talla

A farkon wannan shekarar ne Faransa da Jamus suka matsa wa Rasha lamba kan yarjejeniyar tura mayaka dubu 1 daga kamfanin sojojin haya na Wagner mai alaka da Rasha zuwa Mali da ke fama da rikici.

Ministan Harkokin Wajen Rasha Sergei Lavrov ya ce, sun  fahimci bukatar tallafa wa Mali wajen yaki da ta'addanci a wata tattaunawa da ya yi da takwaransa na Mali Abdoulaye Diop a birnin Moscow.

Lavrov ya ce, suna samar wa kasar kayan aiki da makamai da harsasai, kuma za su yi duk abin da ya dace don dakile barazanar da kasar Mali ke fuskanta.

Ya ce, kamata ya yi a mika tambayoyi kan rawar da sojojin haya na Rasha ke takawa a kasar zuwa ga mahukuntan kasar Mali, kuma matakan soji da 'yan kasar Rasha masu zaman kansu suka kafa ba aikin Rasha ba ne.

Ya kara da cewa idan aka kulla wadancan kwangilolin da halastattun gwamnatocin kasashe masu cin gashin kansu, ban fahimci abin da ake iya gani mara kyau ba game da hakan.

Rahotanni sun ce, yarjejeniyar na zuwa ne a daidai lokacin da Faransa ke shirin rufe sansanoni a Mali inda sojojinta ke yaki da masu kaifin kishin Islama tun shekara ta 2013, sai dai abin da bayanai ke cewa a yanzu shi ne, rikicin sojan da ya kunno kai tsakanin wadannan kasashe na da alaka da rikice-rikice a Ukraine, Afirka da kuma Gabas ta Tsakiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.