Isa ga babban shafi
AMURKA

Amurka zata wanke wadanda aka daure saboda kashe Malcolm X

Hukumomin Amurka na shirin wanke wasu mutane biyu da aka samu da laifin kashe fitaccen mai kare hakkin Bil Adama Malcolm X a shekarar 1965 saboda abinda suka kira kuskure wajen yi musu shari’a.

Malcolm X a shekarar 1963
Malcolm X a shekarar 1963 © AFP
Talla

Ana saran yau Babban lauyan Manhattan, Cyrus Vance ya jagoranci taron manema labarai inda zai sanar da wanke mutanen biyu Muhammad A. Aziz da Khalil Islam.

An daure Aziz mai shekaru 83 rai da rai a shekarar 1966, amma kuma sai aka sake shi a shekarar 1985, yayin da aka saki Islam a shekarar 1987, ya kuma rasu a shekarar 2009.

'Yar Malcolm X Ilyasah Shabazz lokacin da take ganawa da manema labarai a ranar 20 ga watan Fabarairun shekarar 2021 a birnin New York
'Yar Malcolm X Ilyasah Shabazz lokacin da take ganawa da manema labarai a ranar 20 ga watan Fabarairun shekarar 2021 a birnin New York David Dee Delgado GETTY IMAGES NORTH AMERICA/AFP/File

Vance yace ba’a yiwa mutanen biyu adalci ba lokacin da aka musu shari’a aka kuma daure su, saboda haka ya dace su amsa kuskuren da suka yi wajen shari’ar.

Jaridar New York Times ta ruwaito cewar bayan wani sabon bincike na watanni 22 da aka gudanar, ofishin Babban lauyan gwamnati da lauyoyin mutanen biyu sun gano cewar masu gabatar da kara da hukumar FBI da kuma ofishin ‘Yan Sandan New York sun boye shaidun dake iya wanke mutanen biyu lokacin da aka musu shari’ar.

Wani mutum na 3 da aka tuhuma da kisan, Mujahid Abdul Halim mai shekaru 80 ya amsa kashe Malcolm X, kuma ya shaidawa kotu cewar Aziz da Islam basu da hannu wajen aikata kisan da akayi ranar 21 ga watan Fabarairun shekarar 1965 lokacin da Malcolm X ke shirin gabatar da jawabin sa a Manhattan, amma sai masu gabatar da kara suka boye shaidar.

Wannan shari’a ta dauke hankalin mutanen ciki da wajen Amurka, wadanda suke bayyana damuwa akan rashin adalcin da aka yiwa mutanen biyu na shekaru 56.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.