Isa ga babban shafi
KORIYA TA KUDU

Tsohon shugaban Koriya ta Kudu Doo-hwan ya rasu yana da shekaru 90

Tsohon Shugaban kasar Koriya ta Kudu Chun Doo-hwan ya rasu yau yana da shekaru 90 a duniya kamar yadda kafofin yada labaran kasar suka tabbatar.

Tsohon shugaban Koriya ta Kudu Chun Doo-Hwan (a tsakiya)
Tsohon shugaban Koriya ta Kudu Chun Doo-Hwan (a tsakiya) KIM JAE-HWAN AFP/File
Talla

Wani babban jami’in sa Jeong-ki ya shaidawa manema labarai cewar tsohon shugaban ya rasu ne a gidan sa dake birnin Seoul.

Doo-hwan da yayi kaurin suna wajen kama karya irin na mulkin soji, ya taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin Koriyar da kuma jagorancin gasar Olympics da akayi a shekarar 1988, kafin ya sauka daga mukamin sa sakamakon zanga zangar adawa da shi.

Lokacin da aka yiwa Chun Doo-Hwan shari'a
Lokacin da aka yiwa Chun Doo-Hwan shari'a POOL AFP/File

Tsohon shugaban wanda Janar ne na soji, ya karbi ragamar jagorancin Koriya ne bayan juyin mulkin da ya hallaka shugaba Park Chung-hee a shekarar 1979, yayin da ya jagoranci kasar tsakanin shekarar 1980 zuwa 1988.

A shekarar 1996 kotu ta same shi da laifin cin amanar kasa inda aka yanke masa hukuncin kisa sakamakon tura sojoji domin murkushe masu bore a Gwangju, amma da ya daukaka kara sai aka sauya hukuncin zuwa dauri, yayin da daga bisani shugaban kasa ya masa afuwa.

Alkaluma sun nuna cewar akalla mutane kusan 200 suka mutu lokacin da sojoji suka afkawa masu zanga zangar, yayin da kungiyoyin fararen hula suka ce adadin ya ribanya haka har sau 3.

Bayan rasuwar sa fadar shugaban kasar ta bayyana takaici akan yadda Chun yaki neman gafara akan kisan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.