Isa ga babban shafi
Amurka - NASA

NASA ta harba kumbon sama jannati don dagargaza wasu duwatsu dake samaniya

Hukumar binciken sararin Samaniya ta Amurka ta tura mutane sararin samaniya don aikin dagargaza wasu manyan duwatsu dake rataye a sararin samaniya, sakamakon fargabar cewa idan aka bar su nan da shekaru 50 zasu iya rikitowa su kuma yiwa duniya mummunar illa.

Wani kumbon sama jannati da Amurka ta harba sararin samaniya, 23/11/21.
Wani kumbon sama jannati da Amurka ta harba sararin samaniya, 23/11/21. © Bill Ingalls/NASA via AP
Talla

Bisa al’ada dai su irin wannan manyan Duwatsu dake rateye a sararin samaniya kan shafe shekaru a haka, kafin daga bisani zafin rana ya narka su, su zama kananu sai su fado wannan duniya, wanda kuma duk da hakan sukan yi banna da kisan jama’a.

Wannan ta sa Amurka ta aika masana sararin samaniya don aikin narka wadannan manyan duwatsu da kuma sako su duniya ta hanyar da ba zasu yi barna ba, bayan da aka gudanar da bincike da kuma gano cewa matukar aka bar su a haka, nan da shekaru 50 zasu fado a adadi mai yawa su kuma yi mummunar bannar da duniya bata taba gani ba.

Tawagar masanan dai ta bar wannan duniya ne zuwa sararin samaniya da misalin karfe 10:21 na safiyar wannan Laraba, don gudanar da aikin tarar da su, wanda kuma akayi ittikafin tsakanin su da wannan duniya ta kai nisan tafiyar Kilomita miliyan 11.

Wannan dai bashi ne karon Farko da jami’an hukumar ke zuwa wannan waje ba, amma dai wannan shine karon farko da zasu gudanar da irin wannan aiki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.