Isa ga babban shafi
BALLON D'OR

Messi da Lewandoski da Benzema na takarar Bllon d'Or ta bana

Yau ake bikin bada kyautar ‘dan wasan kwallon kafar da yafi kowa fice a duniya wanda ake kira Ballon d’Or wanda zai gudana a birnin Paris dake kasar Faransa.

Lionel Messi bayan lashe gasar Copa America
Lionel Messi bayan lashe gasar Copa America CARL DE SOUZA AFP/File
Talla

Rahotanni sun ce akwai alamun ‘dan wasan kungiyar PSG Lionel Messi na iya sake lashe kyautar a karo na 7 saboda rawar da ya taka wajen taimakawa kasar sa lashe gasar cin kofin kudancin Amurka da kuma samun tikitin zuwa cin kofin duniya.

Sai dai wasu na kallon Robert Lewandoski da Karim Benzema a matsayin wasu manyan wadanda ke takara da shi wajen lashe wannan kyauta.

 Robert Lewandowski na kungiyar Bayern Munich
Robert Lewandowski na kungiyar Bayern Munich Tobias SCHWARZ AFP/Archives

Jaridar L’Equipe da ake wallafawa a Faransa ta bayyana bikin na yau a matsayin wanda aka dade ana jira bayan jinkirin da aka samu bara sakamakon annobar korona wadda ta hana gudanar da shi.

Messi ya bayyana cewar sake lashe kyautar a wannan shekara zai zama tarihi, amma kuma ace shine ya samu kyautar har sau 7 zai zama alamar rashin hankali.

Karim Benzema bayan jefawa Faransa kwallo a karawar su da Kazakhstan
Karim Benzema bayan jefawa Faransa kwallo a karawar su da Kazakhstan FRANCK FIFE AFP/Archives

‘Dan wasan gaba na Real Madrid Karim Benzema na daga cikin wadanda ake hasashen suna iya lashe kyautar bana saboda rawar da ya taka a kungiyar sa da kuma taimakawa kasar Faransa samun tikitin zuwa gasar cin kofin duniya da za’ayi shekara mai zuwa a Qatar, duk da ficewar da Faransa ta yi a gasar Euro a zagaye a biyu.

Sai dai wasu na kallon matsalar da Benzema ya samu a kotu wadda tasa aka masa daurin jeka ka gyara halin ka na shekara guda na iya tasiri wajen takarar ta sa na lashe kyautar.

Robert Lewandoski na cikin wadanda wasu ke kallon cewar yana iya samun nasara lashe kyautar saboda tarihin da yake ci gaba da rubutawa da kungiyar sa ta Bayern Munich.

Cristiano Ronaldo baya takarar bana
Cristiano Ronaldo baya takarar bana Ian KINGTON AFP/File

Masu sanya ido akan harkar kwallon kafa sun bayyana cewar babu wanda ya dace ya lashe kyautar bara da ya wuce Lewandoski amma sai cutar korona ta hana gudanar da bikin.

‘Dan wasan gaba na kungiyar Chelsea Jorginho wanda ya lashe duk wani kofi dake nahiyar Turai na daya daga cikin wadanda suma ake ganin suna iya lashe kyautar.

Daga bangaren mata kuwa akwai ‘yar wasa Alexia Puttelas wadda ta lashe kofin zakarun nahiyar Turai da kuma lambar kyautar ‘yan wasar da tafi fice wadanda ke kasa da shekaru 21.

A bana 'dan wasan gaba na Portugal da Manchester United Cristiano Ronaldo bayan cikin wadanda ake saran su lashe kyautar saboda rashin lashe kofuna da kuma kai kasar sa gasar cin kofin duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.