Isa ga babban shafi
Corona-Omicron

Babu tabbacin rigakafinmu ya yi tasiri kan nau'in Omicron- Moderna

Kamfanin Moderna da ke jerin kamfanonin da ke aikin samar da rigakafin covid-19 ya ce bashi da tabbacin nau’in rigakafinsa ya iya tasiri kan sabon nau’in cutar na Omicron da ke ci gaba da zama barazana bayan yaduwarsa a kasashe da dama.

Rigakafin corona samfurin Moderna.
Rigakafin corona samfurin Moderna. JOEL SAGET AFP
Talla

Kamfanin Moderna na Amurka ya yi gargadin cewa sabon nau’in covid-19 na Omicron na da saurin yaduwa fiye da hasashe duk da cewa kawo yanzu babu rahoto kan wanda ya kashe.

Stephane Bancel shugabar kamfanin na Moderna a wata zantawarta da Financial Times a yau talata ta ce nan da makwanni biyu ake sa ran kammala tattara bayanai game da zubi ko kuma yanayin nau’in na Omicron sai dai saurin yaduwarta bayan bulla a Turai da kudancin Amurka cikin kasa da mako guda bayan bayyanarta a Afrika ta kudu abin fargaba ne matuka.

A cewar Stephane duk zantawarta da masana kimiyya game da sabon nau’in na Omicron su kan bayyana mata matukar fargabarsu kan illar da nau’in ka iya yi.

Hasashen masana dai na ganin mai yiwuwa sabon nau’in na Omicron ya iya bijirewa nau’ikan rigakafin da ake da su yanzu, musamman bayan da Moderna da kansa ya diga ayar tambayar cewa babu tabbacin nau’in rigakafinsa ya iya tasirin yakar Omicron.

Tuni dai kasashen Duniya suka tsaurara matakai ciki har da wadanda suka fara kulle iyakoki duk dai a yunkurin dakile yaduwar nau’in na Omicron da aka samu bullarsa makon jiya a Afrika ta kudu.

Yanzu haka dai kamfanonin da ke aikin samar da rigakafin da suka kunshi Moderna na Amurka da hadakar Pfizer da BioNTech da kuma Sputnik V na Rasha dukkaninsu sun sanar da nisa a bincike kan nau’in na Omicron don samar da kariya.

Moderna ya bayyana cewa da yiwuwar nau’in Omicron ya dara na Delta a hadari tare da zama babbar barazana ga kasashe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.