Isa ga babban shafi
China-Faransa

Faransa ta nesanta kanta da masu kauracewa gasar Olympic a Beijing

China ta gargadi kasashen yammacin Duniya game matakin kauracewa gasar Olympics ta hunturu da za ta gudana a Beijing cikin shekarar 2022, tana mai cewa ko shakka babu kasashen da suka dauki matakin za su biya farashi mai girma, gargadin da ke zuwa dai dai lokacin da Faransa ke nesanta kanta da yunkurin wanda Amurka ke jagoranta.

China ta matukar fusata da matakin Amurka na kauracewa gasar ta Olympics a Beijing.
China ta matukar fusata da matakin Amurka na kauracewa gasar ta Olympics a Beijing. REUTERS - TINGSHU WANG
Talla

Tun farko Amurka ta fara sanar da matakin kauracewa gasar ta Olympics gabanin Australia da Birtaniya da kuma Canada su mara mata baya, yunkurin da ya matukar fusata China wadda ta bayyana shi da rikicin Diflomasiyya.

Sai dai Washington ta kafa hujja da cewa matakin kin aikewa da ‘yan wasanta gasar ta Beijing a 2022 na da nasaba da yadda Chinar ke ci gaba da take dokokin kare hakkin dan adam da kuma kisan kare dangi ga tsirarun kabilar Uyghur da ke yankin Xianjiang.

Ma’aikatar harkokin wajen China ta bakin kakakinta Wang Wenbin ya shaidawa manema labarai cewa matakin kasashen Amurka da Canada da Birtaniya da kuma Australia na shigar da siyasa cikin harkokin wasa mataki da sam Beijing ba za ta dauka kuma za su biya farashi mai girma.

Sai dai a dai dai lokacin da ake samu karuwar kasashen da ke mara baya ga Amurkan wajen kauracewa Beijing 2022, Ma’aikatar ilimi da wasanni ta Faransa ta ce sam baza ta shiga sahun masu kauracewa gasar ba.

Acewar ministan wasannin Faransa Jean-Michel Blanquer akwai bukatar kasashe su rika banbance siyasa da kuma wasanni yana mai cewa kasar za ta ci gaba da caccakar China kan take hakkin dan adam amma hakan bazai sanya ta kauracewa gasar ta Olympic ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.