Isa ga babban shafi
Coronavirus

Yin rigakafi sau uku na maganin Omicron - Pfizer

Kamfanonin BioNTech da Pfizer sun ce, bayar da allurar rigakafin cutar COVID-19 sau uku na kawar da sabon nau’in cutar na Omicron, kamar yadda gwajin da suka gudanar a dakin bincike ya tabbatar, inda suka ce za su iya samar da rigakafin da zai bada kariya ga nau’in Omicron a watan Maris na shekarar 2022 idan akwai bukatar hakan.

Wani mutun na karbar rigakafin Korona a Jamus
Wani mutun na karbar rigakafin Korona a Jamus THOMAS KIENZLE AFP/File
Talla

A sanarwar farko a hukumance da kamfanonin samar da rigakafin suka fitar a kan yiwuwar dakile nau’in Korona na Omicron da alluran rigakafin cutar sau biyu, BoiNTech da Pfizer sun ce allurai biyu sun yi tasiri wajen tasiri a kan cutar, amma karin ta 3 za ta gama da cutar.

Samfurin jinin da aka karba daga wadanda suka karbi rigakafin Covid har sau biyu a wata daya da ya gabata ya nuna yadda cutar ta gaza tasiri kamar yadda alluran 2 suka yaki ainihin cutar ta Covid-19 da aka fara ganowa daga China.

A wata sanarwa, shugaban kamfanin Pfizer, Albert Bourla ya ce duk da cewa mutane da dama a Turai sun karbi rigakafin a karo na biyu, abu mafi alfanu shi ne karbar karin na 3 don dakile yaduwar cutar.

Duk da cewa ba a tantance wajibcin samar da wani rigakafi na dabam don yakar nau’in Omicron na cutar Covid-19 ba, kamfanonin sun ce, za su ci gaba da kokarinsu na lalubo rigakafin da za ta bada kariya ga sabon nau’in cutar, wanda suka fara tun ranar da masana kimiyya suka bayyana damuwar bayyanar Omicron din a 25 ga Nuwamba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.