Isa ga babban shafi
Amurka-Assange

Amurka ta samu nasara kan mutumin da ya tona asirinta

Gwamnatin Amurka ta yi nasara a karar da ta daukaka domin kalubalantar hukuncin wata kotun birnin London wadda ta hana tasa keyar mu’assasin shafin tonon silili na Wikileaks, Julian Assange daga Birtaniya.

Julian Assange
Julian Assange Justin TALLIS AFP/File
Talla

Hukumomin Washington sun kalubalanci hukuncin da aka yanke a cikin watan Janairu da ke cewa, akwai yiwuwar Assange mai shekaru 50 ya kashe kansa da zarar an tasa keyarsa zuwa Amurka domin fuskanta shari’a.

Gwamnatin Amurka na son Assange ya fuskanci shari’a saboda yadda ya fallasa wasu bayanan sirri na sojojinta a shekarar 2010, bayanan da ke da nasaba da yakin da Amurka ta yi a Afghanistan da Iraqi.

A cikin watan Otoban da ya gabata, aka yi zaman sauraren shari’a na tsawon kwanaki biyu, inda lauyoyin Amurka suka yi jayayyar cewa, ainihin alkalin da ya jagoranci zaman bai bai wa sauran kwararru cikakkiyar damar gabatar da hujjoji game da lafiyar kwakwaluwar Assange ba.

Kazalika kwararrun sun bai wa kotun tabbacin cewa, ba za a tsare Assange a wani kebantaccen gidan yarin azabtarwa ba, sannan kuma za a ba shi cikakkiyar kulawa.

Yanzu haka alkalai biyu a babbar kotun birnin London sun amince da tabbacin da Amurka ta bayar na cewa, Assange ba zai fuskanci tsauraran matakai ba kafin tuhumarsa ko kuma bayan haka.

Kazalika Amurka ta yi alkawarin tasa keyarsa zuwa Australia da zarar ta kammala yi masa shari’a.

Sai dai tuni budurwarsa, Stella Moris ta ce, lallai za ta daukaka kara domin kalubalantar nasarar da Amurka ta samu a kan Assange, inda ta bayyana hukuncin kotun a matsayin rashin adalci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.