Isa ga babban shafi
BIRTANIYA

Birtaniya ta janye dokar hana 'Yan Najeriya da wasu kasashe zuwa kasar

Sakamakon matsin lamba daga ciki da wajen Birtaniya, hukumomin kasar  sun soke dokar haramtawa baki daga wasu kasashen duniya 11 ziyarar kasar saboda dakile yaduwar cutar korona nau’in Omicron.

Firaministan Birtaniya Boris Johnson
Firaministan Birtaniya Boris Johnson AP - Kirsty O'Connor
Talla

Sakataren lafiya Sajid Javid ya shaidawa majalisar dokoki cewar dokar bata da tasiri ganin yadda nau’in cutar ya yadu a tsakanin mazauna kasar, saboda haka za’a dage ta daga karfe 4 na asubahin gobe laraba.

Daga cikin Kasashen da dokar ta shafa akwai Angola da Botswana da Najeriya da Afirka ta Kudu da kuma Zambia.

Sauran sun hada da Eswatini da Lesotho da Malawi da Mozambique, Namibia da Zimbabwe.

Hukumomin kasar sun ce zasu ci gaba da yiwa bakin dake zuwa Birtaniya daga kasashen waje gwaji da zaran sun sauka a kasar domin gano wadanda suke dauke da cutar.

Kafin wannan mataki, Birtaniya ta bada umurnin cewar duk wani bako da ya fito daga wadannan kasashe zai biya kudin killace kan sa a otel din da gwamnati ta amince da shi na kwanaki 10 da kuma zuwa da shaidar dake nuna cewar an masa gwaji a kasar da ya fito a cikin sa’oi 48.

Rahotanni sun ce baki da dama sun biya miliyoyin kudade domin zama a wuraren da gwamnati ta ware, yayin da ake samun korafi akan ingancin otel din da kuma irin abincin da ake baiwa jama’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.