Isa ga babban shafi

Fararen hula sama da dubu daya suka rasa rayukansu, dalilin kura-kuran Amurka

Wani rahoto da ma’aikatar tsaron Amurka Pentagon ta wallafa, ya nuna cewar dakarun kasar sun tafka kura-kurai wajen tattara bayanan sirri a yakin da suke yi a yankin Gabas ta Tsakiya, abinda yayi sanadin mutuwar dubban fararen hula, ciki har da kananan yara, yayin hare-hare sau sama da dubu 50 da aka kaddamar akansu.

Tambarin ma'aikatar tsaron Amurka ta Pentagon
Tambarin ma'aikatar tsaron Amurka ta Pentagon REUTERS - ALEXANDER DRAGO
Talla

Rahoton ma’aikatar tsaron ta Pentagon da jaridar New Tork Times ta wallafa a ranar Asabar, ya bayanan yadda fararen hula sama da dubu 1 da 300 suka rasa rayukansu, dalilin kura-kuran da Amurka ta tafka wajen kai hare-hare da zummar kashe ‘yan ta’adda ba tare da maida hankali wajen tantance wurare da kuma wadanda take kaiwa farmakin ba.

Jami'in. Hukumar tsaro ta Pentagon a Amurka
Jami'in. Hukumar tsaro ta Pentagon a Amurka © AP Photo/Alex Brandon

Bayanai dai sun ce a yayin da tuni kafafen yada labarai da dama suka ba da rahoton da yawa daga cikin hare-haren da aka kaiwa fararen hula, jaridar ta New York Times ta ce bincikenta ya nuna cewa adadin mutanen da suka rasa rayukan nasu ya nin-ninka wanda aka bayyana.

Jirgi marar matuki na kasar Amurka
Jirgi marar matuki na kasar Amurka © AP - Kirsty Wigglesworth

 

Daga cikin rahotannin kashe fararen hular da Amurka ta yi a yankin Gabas ta Tsakiya akwai wani harin bam da dakarunta na musamman suka kai a ranar 19 ga watan Yulin shekarar 2016 kan wasu wurare da ake zargin sansanonin kungiyar IS ne a arewacin kasar Syria. Rahoton farko da aka bayar bayan kai farmakin ya bayyana kashe ‘yan ta’adda 85 ne, amma daga bisani  aka gano cewar wadanda dakarun na Amurka suka kashe manoma ne da wasu kauyawa, kuma adadinsu ya kai 120.

Wasu daga cikin mutanen da aka ritsa da su
Wasu daga cikin mutanen da aka ritsa da su OMAR HAJ KADOUR AFP/File

A baya-bayan ne kuma, Amurka ta janye ikirarin da ta yi cewa wata mota da wani jirginta mara matuki ya tarwatsa akan titin Kabul cikin watan Agusta na dauke da bama-bamai, domin kuwa an gano cewar mutane 10 ne ‘yan gida daya cikinsu harda kananan yara a cikin motar.

Rahoton ma’aikatar tsaron Pentagon ya kara da cewar, cikin shekaru biyar kawai, sojojin Amurka sun kai hare-hare ta sama fiye da dubu 50,000 a kasashen Afganistan, da Iraqi da kuma Syria.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.