Isa ga babban shafi
Kimiya

An harba na'urar da za ta tattaro bayanan wasu duniyoyin

Na’urar hangen nesa mafi karfi da aka cilla ta  can saman jannati a yau Asabar, ta tarwatse, inda kuma ta doshi mazauninta mai tazarar kilomita miliyan 1.5 daga nan doran kasa.

An lullbe na'urar ta James Webbs a cikin kwanson kumbo na roka
An lullbe na'urar ta James Webbs a cikin kwanson kumbo na roka AFP - BILL INGALLS
Talla

Na’urar ta James Webb wadda aka kashe mata biliyoyin kudi  na Dala wajen kera ta, ta bar wannan doran kasar ne daga cibiyar aikin kimiya ta Kourou da ke yankin Guiana na Faransa.

Ana sa ran wannan na’urar za ta kwashe tsawon wata guda kafin ta isa ainihin mazauninta a can duniyar ‘yan saman jannati.

Masana kimiya na ganin cewa, na’urar ta James Webb za ta taimaka wajen tattaro karin bayanai game da asalin halittu da sauran duniyoyi.

An dai lullube wannan na’urar a cikin kunbon roka saboda girmanta da kuma karfinta  kafin daga bisani a  cilla ta can sararin samaniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.