Isa ga babban shafi
Rasha-Amurka

Putin da Biden za su tattauna ta wayar tarho kan sabanin tsakaninsu

Shugabannin Kasashen Amurka da Rasha sun amince da amfani da diflomasiyya wajen warware rikicin da ke tsakaninsu a tattaunawar wayar tarho da za ta gudana tsakaninsu a yau alhamis, wadda za ta tabo batutuwa da dama ciki har da rikicin Ukraine da bangarorin biyu ke da sabanin ra’ayi akai.

A ranar 27 ga watan nan na Disamba ne shugabannin biyu suka yi wata zantawa ta bidiyon na'ura gabanin ganawarsu ta watan Janairu mai zuwa a Geneva.
A ranar 27 ga watan nan na Disamba ne shugabannin biyu suka yi wata zantawa ta bidiyon na'ura gabanin ganawarsu ta watan Janairu mai zuwa a Geneva. DENIS BALIBOUSE POOL/AFP/File
Talla

Sanarwar fadar Kremlin a Rasha sa’o’i kalilan gabanin tattaunawar ta shugaba Vladimir Putin da Joe Biden na Amurka, wadda ke zuwa bayan ganawar jagororin biyu ta bidiyon na’ura a farkon watan Disamaba ta ce Moscow ta zabi warware rikicin da ke tsakaninta da Washington ta hanyar tattaunawa maimakon ci gaba da takun saka kan batutuwa daban-daban.

Wannan na zuwa bayan tun farkon watan nan Moscow ta mikawa kasashen yammaci bukatunta don tabbatar da tsaro da zaman lafiyar tsakaninsu ciki har da hana kungiyar tsaro ta NATO kara yawan mambobi tsakanin kasashen tsohuwar tarayyar Soviet da kuma kaucewa samar da sansani a gab da ita.

Tattaunawar ta wayar tarho wadda za ta gudana tsakanin Biden da Putin da misalin karfe 9 da rabi na dare agogon GMT, na zuwa ne gabanin ganawar shugabannin biyu ta keke da keke cikin watan Janairu a Geneva dai dai lokacin da Amurka ke nanata bukatar samar da mafita kan rikicin Ukraine a bangaren guda Moscow na ganin tattaunawa kan barazanar tsaron da ta ke fuskanta shi ne mafita ga sabanin fahimtar bangarorin biyu.

Wani babban jami’in fadar White House ya ce Biden na fatan warware rikicin Amurka da Rasha ta fuskar Diflomasiyya, amma hakan baya nufin basu shiryawa tunkarar matsalar ta wata fuskar ba matukar Moscow ta nuna tirjiya.

Shi kansa Shugaba Vladimir Putin da yanzu haka ke tsaka da hutun karshen shekara a mahaifarsa Delaware ya ce a shirye ya ke tattaunar fahimtar juna da girmamawa ta shiga tsakanin kasashen biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.