Isa ga babban shafi
Rigakafin Korona

Kasashe matalauta sun yi watsi da tallafin alluran Korona fiye da miliyan 100

Asusun kula da yar ana Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya ce cikin watan da ya gabata, kasashe matalauta sun yi watsi da alluran rigakafin cutar Korona sama da miliyan 100 da gidauniyar COVAX ke rabawa, saboda yadda alluran ke gaf da gurbacewa.

Wani ma'aikacin lafiyar yankin Falasdinu yayin aikin jigilar alluran. rigakafin Korona 300,000 da asusun UNICEF ya aika ta a karakshin shirin Covax zuwa yankin Salem, kusa da birnin Nablus na Yammacin Kogin Jordan.
Wani ma'aikacin lafiyar yankin Falasdinu yayin aikin jigilar alluran. rigakafin Korona 300,000 da asusun UNICEF ya aika ta a karakshin shirin Covax zuwa yankin Salem, kusa da birnin Nablus na Yammacin Kogin Jordan. Jaafar Ashtiyeh AFP/Archivos
Talla

Babban adadi ya nuna wahalhalun da ke tattare da yin allurar rigakafin a duniya duk da karuwar samar da alluran rigakafin, tare da COVAX yana kusa da isar da alluran rigakafi biliyan 1 ga jimillar kasashe kusan 150.

Babban daraktan sashen samar da kayayyaki a hukumar ta UNICEF Etleva Kadilli ya shaida wa 'yan Tarayyar Turai cewar babban dalilin kasashen marasa karfi na kin karbar tallafin rigakafin na Korona shi ne yadda alluran ke shirin lalacewa nan da ba da dadewa ba.

Babban jami’in na UNICEF ya kara da cewar, akasarin kasashen matalauta na fama da kalubalen tilasta jinkirta rabawa al’ummominsu alluran rigakafi na Korona saboda rashin isassun wuraren ajiya ciki har da na’urar sanyaya kaya ta firji domin adana alluran na rigakafi.

Bayanai daga hukumar UNICEF sun ce yanzu haka akwai alluran allurai akalla miliyan 681 na tallafi da aka yi jigilarsu kasashe matalauta kusan 90, kamar yadda wata kungiyar agaji ta CARE ta tabbatar a baya bayan nan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.