Isa ga babban shafi

Gwamnatin Taliban na neman goyan bayan kasashen Musulmi

Gwamnatin Taliban da ke mulki a Afghanistan, ta bukaci kasashen musulmi da su kasance na farko da za su amince da ita, wanda hakan zai bai wa sauran kasashen duniya damar ci gaba da bai wa kasar taimako a cewarta.

Afghanistan
Afghanistan AFP
Talla

 A shekara ta 2020 Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa Afghanistan na cikin hatsarin fukantar tabarbarewar al’amura, muddin kasashen duniya suka gaza daukar matakan samar da hanyoyin samun kudaden shiga ga kasar.

Majalisar ta ce ya zama dole a tabbatar kudade sun ci gaba da gudana cikin Afghanistan duk da cewar ba a san hakan ya zama taimako kai tsaye ga mayakan Taliban.

Taron Ministocin kasashen wajen Afghanistan da wasu kasashen Duniya
Taron Ministocin kasashen wajen Afghanistan da wasu kasashen Duniya AP

A taron manema labaran da ya gabatar jiya laraba, firaministan kasar Mohammad Hassan Akhund, ya ce duk wani taimako da kasashen duniya za su bai wa Afghanistan ba wai zai je ne a aljiuhun ‘yan Taliban ba, sai dai domin amfanin al’ummar kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.