Isa ga babban shafi
China-Amurka-WTO

Amurka ta fusata da hukuncin WTO da ya ba China damar sanya mata haraji

Amurka ta bayyana takaicinta dangane da hukuncin hukumar kasuwanci ta Duniya da ya sahalewa China damar iya lafta mata harajin dala miliyan 645 kan cinikayyarsu a kowacce shekara.

Amurka ta bayyana hukuncin na WTO mai cike da son rai.
Amurka ta bayyana hukuncin na WTO mai cike da son rai. REUTERS - DENIS BALIBOUSE
Talla

WTO ta bai wa China damar daukar fansa wajen karbar harajin har na dala miliyan 645 kan  hajojin da Amurkan ke shigar mata da su kasar a duk shekara, hukuncin da ke biyo bayan rikicin kasuwancin da manyan kasashen biyu mafiya karfin tattalin arziki suka jima suna yi da junansu.

Wasu bayanai na nuna cewa an kai ga wannan matsaya ne bayan tafka doguwar muhawara a mabanbantan lokaci da ya kai ga sahale wannan mataki.

Sai dai bayan tsayar da adadin harajin China ta nemi hukumar sasanta rikicin kasuwanci ta shiga tsakani don dakile duk wata barazana da ka iya sauya hukuncin na harajin dala miliyan 645.

Tuni hukumar kasuwanci ta Amurka ta bayyana matukar damuwa a hukuncin da ta kira mai cike da rashin adalci tare da bayyana aniyarta ta samar da mafita.

Tun a shekarar 2012 kasashen biyu suka fara takaddama kan harajin ko da ya ke zuwa Donald Trump mulkin Amurka ya mayar da takaddamar zuwa gagarumin rikici ta yadda bangarorin biyu suka rika musayar manyan haraji tsakaninsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.