Isa ga babban shafi
Rasha-NATO

Kassahen yamma sun yaba da fara janyewar dakarun Rasha daga Ukraine

Shugabannin kasashen yammacin duniya sun ce sun fara ganin alamun da ke nuna cewa Rasha za ta sassauta yunkurinta game da rikicin Ukraine, bayan da fadar Kremlin ta sanar da janye wasu sojojin da aka girke a kan iyakokin makwabciyarta.

Yadda wasu dakarun Rasha ke komawa gida.
Yadda wasu dakarun Rasha ke komawa gida. via REUTERS - COLLECTIVE SECURITY TREATY ORGAN
Talla

Shugabannin kasashen yammacin duniya sun zargi Rasha dai da sanya sojojin tun kafin yuwuwar kutsawa yammacin Ukraine, inda suka yi gargadin cewa duk wani hari da zata kai shakka babu za ta fuskanci takunkumin tattalin arziki mai tsanani.

Bayan ganawarsa da shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz a birnin Moscow, shugaba Vladimir Putin ya ce Rasha tabbas ba ta son yaki, kuma a shirye take ta lalubo bakin zaren warware rikicin kasashen yammacin duniya.

Shugaban na Jamus ya bi sahun sauran kasashen yammacin duniya wajen bayyana fatan ganin an dauki matakan dakile rikicin.

Shugaban kungiyar tsaro ta NATO Jens Stoltenberg ya ce a Brussels har yanzu ba a samu alamar tabarbarewar yarjejeniyar da aka yi ba amma akwai wasu dalilai na kyakkyawan fata, yayin da Firayim Ministan Biritaniya Boris Johnson ya ce akwai alamun kulla huldar diplomasiyya da Rasha, amma bayanan da ke nuna yiwuwar mamaye Ukraine har yanzu ba su da kwarin gwiwa a kai.

Rikicin mafi muni tsakanin Rasha da kasashen Yamma tun bayan kawo karshen yakin cacar-baka ya kai kololuwa a wannan makon, inda Amurka ta yi gargadin cewa za a iya kai wani gagarumin farmaki, ciki har da kai hari kan birnin Kyiv, cikin 'yan kwanaki.

Ma'aikatar tsaron Rasha ta sanar da janye wani rukuni na sojojinta, tana mai cewa wasu dakarun da aka tura kusa da Ukraine sun kammala atisayen da suke yi kuma suna tattara kayansu domin janyewa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.