Isa ga babban shafi
EU-Afrika

EU na taro da shugabannin Afrika

A yau Alhamis ne shugabannin kasashen Turai ke ganawa da takwarorinsu na nahiyar Afrika a wani taron kwanaki biyu da ke gudana a birnin Brussels wanda aka shirya da zummar yaukaka alaka tsaknin banbagrorin biyu.

Wasu daga cikin shugabannin Turai
Wasu daga cikin shugabannin Turai AP - Olivier Matthys
Talla

Ana sa ran shugabannin za su cimma yarjeniyoyi da dama a fagen kasuwanci a daidai lokacin da kasashen Rasha da China ke rige-rigen fadada hajojinsu a nahiyar ta Afrika.

Abubuwan da wannan taro ke tattaunawa a kai sun hada da batun zuba jari da samar da roia-kafin Korona da matsalar kwararen baki da kuma girke sojin haya a Afrika, sai kuma yawaitan juyin mulki da ake gani a baya-bayan nan a nahiyar ta Afrika.

Wannan na zuwa ne a yayin da kungiyar kasashen Turai ke shan caccaka kan yadda take noke riga-kafin Korona da ake ganin ka iya taimaka wa Afrika wajen shawo kan annobar, inda EU din ta fi mayar da hankali wajen safarar rigakafin zuwa kasashe mawadata.

Yanzu haka dai EU na son yawaita kudaden da take bai wa Afrika domin inganta bangaren kiwon lafiyarta musaman dangane da samar da alluran rigakafin Korona.

A bangare guda, wannan taro na fatan cimma matsaya game da zuba jari mai yawa a Afrika ta yadda nahiyar za ta karkata hankalinta kan hajojin EU fiye da na China kamar yadda masana suka yi fashin baki.

Gabanin taron dai, Shugabar Kungiyar Tarayyar Turai, Ursula von der Leyen ta  bayyana cewa, suna son zuba jarin fiye da Euro biliyan 150 a nahiyar ta Afrika nan da shekara ta 2027.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.