Isa ga babban shafi
Rasha-Ukraine

Barazanar nukiliyar Rasha ne ya hana kasashe shiga yakin Ukraine- ICAN

Kungiyar ICAN ta bayyana barazanar da shugaba Vladimir Putin ya yiwa kasashen yammaci da makamin nukiliya a matsayin mai cike da hadari, inda ta bukaci kasashe su mara mata baya wajen ganin duniya ta zauna ba tare da irin wannan makami ba. Wannan kira na zuwa dai dai lokacin da mamayar Rasha a Ukraine ta shiga kwana na 14 lamarin da ya haddasa kwararar ‘yan gudun hijira fin miliyan 2 baya ga rasa rayukan dakaru fiye da dubu 5.

Kwanaki kalilan bayan mamayar Rasha a Ukraine ne shugaba Vladimir Putin ya umarci sashen nukiliyar kasar ya kasance cikin shirin ko ta kwana.
Kwanaki kalilan bayan mamayar Rasha a Ukraine ne shugaba Vladimir Putin ya umarci sashen nukiliyar kasar ya kasance cikin shirin ko ta kwana. AP - Alexander Zemlianichenko
Talla

Gungun ICAN da ya lashe kyautar Nobel ya yi ikirarin cewa shugaba Vladimir Putin na Rasha ya yi amfani da barazanar nukiliyar nr wajen hana kasashen yammacin shiga yakin da ya ke da Ukraine, batun da kungiyar ke cewa idan da kasashe sun mutunta kira-kirayenta wajen kwance makaman nukiliyar da suka mallaka ko shakka babu ba za a kai ga wannan mataki ba.

Beatrice Fihn da ke jagorancin gungun na ICAN da ya shafe shekaru yana fafautukar yaki da mallakar makamin nukiliya, ya ce barazanar ta Putin shi ne lokaci mafi ban tsoro ba kadai ga kasashen yammaci da suka yi yunkurin shiga yakin ba, har ma da sauran daidaikun kasashe.

Kwanaki kalilan bayan Putin ya fara mamayar Ukraine ne ya bukaci sashen nukiliyar kasar ya kasance cikin shirin ko ta kwana, batun da ya tayar da hankalin Duniya.

Dai dai lokacin da yakin ke shiga kwana na 14 ma’aikatar tsaron Amurka ta bayyana cewa, mamayar ta Putin ba ta tafiya kamar yadda ya yi hasashe domin kuwa zuwa yanzu ya yi asarar dakarun da yawansu yakai dubu 2 zuwa 4, baya ga manyan takunkuman karya tattalin arziki da ya janyowa Rashan, inda shugaba Joe Biden ke cewa tabbas abu ne mai sauki ga Putin ya iya kwace Ukraine amma zai zame masa abu mai matukar wahala iya ci gaba da rike tasa kasar.

Zuwa yanzu alkaluma na nuna yadda wannan yaki ya haddasa kwararar ‘yan gudun hijira akalla miliyan 2 zuwa kasashen yammaci, ciki har da ayarin farko na fararen hula daga birnin Sumy da Rasha ta taimaka wajen kwashesu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.