Majalisar Dinkin Duniya za ta yi taruka kan rikicin Rasha da Ukraine
Majalisar dinkin duniya za ta gudanar da jerin taruka a wannan mako a kan rikicin Rasha da Ukraine, sai dai babu wani karin haske a kan ko za a kai ga amincewa da wani daftari a hukumance.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Majiyoyin diflomasiya sun shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa cewa a ranar Litinin, kwamitin tsaro na majalisar za ta tattauna batun tsarin tsaro a Turai, inda ake sa ran ministan harkokin wajen Poland, Zbigniew Rau ya gabatar da jawabi a yayin taron.
Duk da cewa taro ne na shekara shekara, zai mayar da hankali ne a kan yakin da ake a Ukraine, kuma mai yiwuwa ya sabanta kiraye kirayen lalubo zaman lafiya.
Kamfanin dillancin labaran Faransa ya ruwaito cewa ya jiyo wasu majiyoyi na dabam na cewa kwamitin zai duba batun matsalar jnkai a Ukraine, tare da yin tir da kai wa yankunan fararen hula hare hare.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu