Isa ga babban shafi
Rasha-tattalin Arziki

Rasha na barazanar kwace wasu kamfanonin kasashen yammaci

Hukumomin Rasha da ke fuskantar takukuman tattalin arziki daga kasashen yamma, sun mayar da martani ta hanyar barazanar kwace wasu kaddarori mallakin kasashen da kuma dakatarwa, kamar yadda jaridar Wall Street Journal ta ruwaito.

Shugaba Vladimir Putin na Rasha.
Shugaba Vladimir Putin na Rasha. AP - Alexander Zemlianichenko
Talla

A cewar wata majiya, masu gabatar da kara a Rasha sun gargadi kamfanonin ta hanyar kira a waya da wasika da kuma ziyarar kafa da kafa don isar musu da gargadin.

Sai dai a ranar Lahadi ofishin jakadancin Rasha a Amurka ya karyata rahoton.

Rasha dai na fuskantar takunkumi daga gwamnatocin yammaci tun bayan mamayar da ta yiwa Ukraine, lamarin da ya sa wasu kamfanoni ke bayyana dakatar da ayyukan su a kasar.

Sai dai kamfanonin Coca-Cola, McDonald’s da Procter & Gamble da kuma Yum Brands ba su amsa bukatar da kamfanin dillancin labarai na AFP ya mika musu ba akan batun ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.