Isa ga babban shafi
Guatemala-Mata

Guatemala ta janye dokar dauri ga matan da suka zubar da ciki

Majalisar dokokin Guatemala ta janye sabuwar dokar da ta tanadi daurin gidan yari ga duk matar da ta zabi zubar da ciki baya ga haramta auren jinsi, kwanaki kalilan bayan zartas da ita.

Matan da ke zanga-zangar bukatar janye dokar zubar da ciki da kuma wadda ta haramta auren jinsi.
Matan da ke zanga-zangar bukatar janye dokar zubar da ciki da kuma wadda ta haramta auren jinsi. AP - Oliver de Ros
Talla

Majalisar ta Guatemala mai rinjayen masu ra’ayin ‘yan mazan jiya, yayin zamanta na yau laraba ta yi watsi da sabuwar dokar makwanni kalilan bayan zartas da ita wadda ta haddasa cece-kuce a sassan kasar ta kudancin Amurka.

Shugaba Alejandro Giammattei a makon jiya ne ya bukaci watsi da dokar tare da shan alwashin kalubalantarta idan ta iso teburinsa a wani yunkuri na ganin bata yi karantsaye ga kundin tsarin mulki da kuma dokokin kasa da kasa da Guatemala ta sanyawa hannu ba.

Wata sanarwa da majalisar ta fitar kuma aka wallafa a jaridun kasar ta sanar da cewa matakin janye sabuwar dokar mai cike da sarkakiya ya biyo bayan doguwar tattaunawa tsakanin ‘yan majalisun kasar.

Dokar wadda aka yiwa lakabi da kariyar Iyali na da nufin daurin shekaru 10 sabanin 3 da aka saba gani a kasar ga duk macen da ta zubar da ciki wanda ke nufin karin ladabtarwa ga matan da ke da dabi’ar ta zubar da cikin ko kuma bayar da dakon ciki ga wata mace daban.

Karkashin dokokin Guatemala mace na iya zubar da ciki ne kadai idan rayuwarta na cike da hadari.

A ranar mata ta duniya da ta gudana 8 ga watan Maris din da muke ciki ne Majalisar ta Guatemala ta zartas da dokar wadda ta kuma haramta auren jinsa da kuma haramta koyar da ilimin auratayyar jinsi guda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.