Isa ga babban shafi

Kasashen Turai sun sauya matsaya kan bakin-haure

Yakin Ukraine da Rasha ya tilastawa kasashen yankin tsakiyar Turai sauya manufofinsu kan bakin-haure, inda a yanzu haka suke ci gaba da karbar adadin ‘yan gudun hijira da ba a taba gani ba daga Ukraine da yaki ya daidaita

Wasu da yakin Ukraine ya raba da muhallansu
Wasu da yakin Ukraine ya raba da muhallansu REUTERS - VLADISLAV CULIOMZA
Talla

A shekarun baya, an sha yin Allah-Wadai da akasarin kasashen na tsakiyar nahiyar Turai kan kin karbar bakin-haure daga Gabas ta Tsakiya da kuma Afirka, a lokacin da matsalar bakin haure a shekarar 2015 da ta kai ga kwararar 'yan gudun hijira sama da miliyan guda zuwa kasashen da suka hada da, Jamhuriyar Czech, Hungary, Poland da kuma Slovakia, abinda ya fusata kungiyar Tarayyar Turai, saboda yadda suka ki amincewa da tsarin rarraba bakin hauren a tsakaninsu.

Sai dai tun bayan da Rasha ta mamaye kasar Ukraine a ranar 24 ga watan Fabrairu, tsoffin kasashen na ‘yan guruguzu da suka kasance karkashin ikon tsohuwar tarayyar Soviet har zuwa 1989, a halin yanzu ba su yi kasa a gwiwa ba wajen taimakawa miliyoyin ‘yan Ukraine da suka tsere daga yakin da Rasha ta kaddamar kansu.

Masu sharhi sun bayyana kusancin al'adu, harshe da yanki na Ukraine daga cikin abubuwan da suka haifar da sauyin manufar, kazalika akasarin 'yan gudun hijirar mata ne masu kananan yara.

Fiye da 'yan Ukraine miliyan uku ne suka bar kasarsu ta makwaftan kasashe da suka hada da Slovakia, da Hungary, da Romania, da Moldova da kuma Poland, wadda ita kadai ta karbi 'yan gudun hijira kusan miliyan biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.