Isa ga babban shafi
Ranar Ruwa ta Duniya

Ruwan da ke karkashin kasa ya ishi duniya baki daya

Majalisar Dinkin Duniya ta jadadda cewa albarkar ruwa da ke kwance a karkashin kasa, wanda Dan Adam zai iya shan sa cikin koshin lafiya, na da matukar yawan da zai ishi al’ummar duniya matukar aka  bi hanyoyin da suka dace.

Har yanzu akwai dimbin al'ummar duniya da ke fama da karancin ruwa a yankunansu
Har yanzu akwai dimbin al'ummar duniya da ke fama da karancin ruwa a yankunansu AFP - SAJJAD HUSSAIN
Talla

Asusun Bunkasa Ilimi, Kimiyya da Raya Al’adu na Majalisar Dinkin Duniya UNESCO ne ke wadannan kalamai, a wani bangare na bukukuwan ranar ruwa ta duniya da ake gudanarwa duk ranar 22 ga watan Maris din kowacce shekara.

Ta cikin wani rahoto da ausun ya fitar, ya ce kaso 99 na dukannin narkakken abu dake karkashin kasa, ruwa ne, duk da cewa akwai karancin wannan ilimi a tsakanin al’ummar duniya.

Bayanin rahoton ya kuma ci gaba da cewa nan da shekaru 30 masu zuwa bukatar tsaftataccen ruwa zai karu, la’akari da karuwar jama’a da kuma masana’antu da habbakar ayyukan gona, wadanda dukannin bangarori ne masu zuwa.

Ko da yake karanto rahoton, Daraktan UNESCO Audrey Azoulay ya ce, sauyin yanayi da gurbacewar muhalli, na busar da ruwan a doron duniya, a don haka akwai bukatar a gaggauta mayar da hankali wajen amfanar wanda ke boye karkashin kasa.

Azoulay ya kuma kara da cewa babbar matsalar a yanzu ita ce hukumomi ba su fara ankara da matsalar ba, wadda kuma za ta yi wa duniya muni idan ba a fara tunkarar ta tun yanzu ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.