Isa ga babban shafi
Amurka

Fursunonin Amurka za su fara samun tabarruki kafin mutuwarsu

Kotun Kolin Amurka ta goyi bayan ‘yancin fursunoni na samun tabarrukin shugabannin addini gabanin zartar musu da hukuncin kisa.

Gadon da ake kwantar da fursunan da ke shirin bakwantar lahira.
Gadon da ake kwantar da fursunan da ke shirin bakwantar lahira. AP - Anonymous
Talla

Hukuncin kotun na zuwa ne bayan wani fursuna ya daukaka kara, inda ya ce, yana son fasto dinsa ya taba shi tare da yi masa addu’a, a daidai lokacin da ake zartar masa da kisan.

A wani kudiri da ya samu amincewar alkalai 8 ciki 9, kotun kolin ta Amurka ta yi watsi da matakin hukumomin da ke kula da gidan yarin Texas na haramta taba fursunan da ke kan gadon aika shi lahira.

John Ramirez, mai shekaru 37, shi ne fursunan da ya kalubalanci matakin hukumomin gidan yarin na Texas, a yayin da ake shirin zartas masa da kisan a ranar 8 ga watan Satumba mai zuwa sakamakon laifin da ya aikata na kashe wani akawun katafaren kanti a 2004, lokacin da ya yi masa fashi.

Shi dai Ramirez ya nemi dakartar da kisan da za a yi masa, yana mai fakewa cewa, lallai sai an bai wa fasto dinsa izinin taba shi a yayin yi masa addu’a kai tsaye a daidai lokacin da ake tsikara masa allurar guba da za ta aika shi lahira.

Gidan yarin Texas dai, ya yarce wa jagororin addini da su rika kasancewa tare da fursunoni a yayin aika su lahira, amma da sharadin yin tsit, sannan kuma ba tare da mika hannayensu domin taba masu laifin ba.

Yanzu dai kotun ta saurari bukatar ta Ramirez, inda daya daga cikin alkalan kotun ya ce, akwai kwararan shedun da  ke tabbatar da ingancin imanin wannan fursuna na ganin cewa, taba mutun a yayin yi masa addu’a na cikin tsarin addini.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.